Saturday 31 January 2026 - 00:38
Ayatullahil Uzma Khamenei Shi Ne Hasken ido Kuma Bugun Zuciyar Raunanan Duniya

Hauza/ Hujjatul Islam Muhammad Yaqoob Bishawi, a cikin wata sanarwa, ya yi Allah wadai da munanan maganganun Donald Trump game da babban jagoran juyin juya halin Musulunci, inda ya ce: "Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Khamenei shi ne hasken ido da bugun zuciyar raunanan duniya, alhali kuwa Trump shi ne mai kashe bil'adama kuma mutumin da aka fi ƙi.

A cewar rahoton sashen fassara na Ofishin Yada Labaran Hauza, Hujjatul Islam Muhammad Yaqoob Bishawi, wani masani kuma malami mai wa'azi na Pakistan, a cikin wata sanarwa, ya yi Allah wadai da munanan maganganun Donald Trump game da babban jagoran juyin juya halin Musulunci, kuma ya ce: "Ayatullahil Uzma Sayyid Ali Khamenei shi ne hasken ido da bugun zuciyar raunanan duniya, alhali kuwa Trump ya kasance makashin bil'adama kuma mutum wanda aka fi yiwa ƙiyayya."

Ya ci gaba da bayyana cewa: "A yau, da wata kalma daga jagoran juyin juya halin Musulunci, 'ya'yan tauhidi a duk faɗin duniya za su iya dakile muguwar siyasar Amurka. A haƙiƙa, Amurka tana tsoron wannan tsarin rayuwa na Allah, wanda aka aiko don kawar da Fir'aunan kowane zamani."

Wannan masanin dan Pakistan ya kara da cewa: "Jagoran juyin juya halin Musulunci mutum ne wanda ya dogara da tunanin Alkur'ani, kuma yana ƙoƙari musamman wajen ceton marasa galihu na Gabas ta Tsakiya daga cin zarafin Amurkawa, kuma a wannan hanyar yana yin kowane irin sadaukarwa."

Hujjatul Islam Wal Muslimin Yaqoob Bishawi, a ƙarshe, yana mai nuni ga sadaukarwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ya ce: "Abin da ke faruwa a Iran a yau, alama ce ta son addinin Musulunci na iyalan gidan Annabi da mabiyan Annabi (SAWA) na gaskiya. Muna jiran ranar da za ta kawar da Fir'aunoni da tsarin mulkin zalunci da ƙasashe masu zalunci, kamar yadda Annabi Musa (A.S.) ya yi."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha